May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sarkin Dutse Nuhu Muhammad Sunusi ya rasu

1 min read

Allah ya yi wa Sarkin Dutse, Nuhu Muhammad Sunusi rasuwa.

Kwamishinan ayyuka na musamman a Jihar Jigawa Auwal Danladi Sankara ne ya tabbatar wa BBC da rasuwar sarkin.

Sarkin ya rasu ne a Abuja bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya kuma ya rasu yana da shekara 79.

Sakatare na musamman na marigayin Wada Alhaji Dutse ya tabbatar wa BBC cewa ana sa ran yin jana’izar sarkin ne a ranar Laraba a Dutse.

Kafin rasuwarsa, sarkin ya taɓa zama Uban Jam’iar Jihar Sokoto wato Sokoto State University.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *