May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

CBN ya umarci bankuna su rika biyan sababbin takardun naira a cikin banki

3 min read

Babban bankin Najeriya CBN ya umarci dukkan bankunan kasuwanci na ƙasar da su fara biyan masu ajiya a bankunan sababbin takardun naira daga cikin bankunan ba kamar yadda ya umarce su da su riƙa biyansu ta na’urar cirar kuɗi ta ATM ba.

Wannan umarnin na zuwa ne bayan da harkokin kasuwanci suka kusan tsayawa cak bayan da gwamnatin Najeriya ta fitar da sababbin takrdun kuɗin na naira 200 da 500 da 1,000.

Cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na bankin Osita Nwanisobi ya sanya wa hannu, CBN ya ce ya lura da wasu miyagun halaye da ‘yan ƙasar ke nunawa na sayarwa, da yin jifa da sababbin takardun kuɗin a iska da tattaka su yayin wasu bukukuwa.

Nwanisobi ya ce babban bankin ya haɗa gwiwa da rundunar ‘yan sandan Najeriya da hukumar tara haraji ta ƙasar da ta EFCC domin hukunta waɗanda aka kama suna taka dokokin ƙasar, musamman waɗanda suka jibanci yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.

Bankin ya kuma gargaɗi ‘yan Najeriya da su guji halayyar wulakanta takardun kuɗin ƙasar musamman a yayin da suke bikin zagayowar ranar haihuwa da na aure da na binne mamata.

Ya ce a ko ina takawa ko kuma wulaƙanta kuɗaɗe ya ci karo da dokar.

Domin kiyaye duk wani shakku, a bayyane yake a cikin sashe na 21 ƙaramin sashe na 3 na dokar CBN wadda aka sauya a 2007 cewa, cukurkuɗa kuɗi ko watsa su ko rawa akansu a lokacin bukukuwa zai iya janyo hukuncin biyan tara ko zaman gidan yari ko kuma duka biyun.

Ka zalika sashe na 21 ƙaramin sashe na 4 ya bayyana cewa “zai iya zama laifin da za a hukunta mutum, duk wanda aka kama yana talla ko sayar da takardun naira ko tsaba ko kuma duk wani nau’i na takardun da CBN yake ɗauka a matsayin kuɗi”.

Mazauna jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya sun koka kan cewa rayuwa ta tsaya cik, sakamakon ƙarancin sabbin takardun kuɗi.

A baya ma gwamnan jihar, Alhaji Maimala Buni ya buƙaci babban bankin kasar da ya jinkirta batun dakatar da karɓar tsoffin takardun naira saboda ƙarancin bankuna a jihar.

Mallam Muhammad Isa Jirgi mai kayan tireda ne a garin Pataskum, wanda ya ce ciniki ya gagara – har an fara rungumar tsohon tsari irin na da can baya wato tsarin ba ni gishiri na ba ka manda.

“Banki babu kuɗi, POS babu kuɗi, wasu ma da yunwa suke kwana, kuma mutane suna tsoron a aika musu ta banki domin sun ce kuɗin ba sa shiga.

“Idan Bafulatani yana so ya sayar da saniyarsa kamar naira 300,000 sai dai ya yi haƙuri ya sayar naira 250,000, akwai wanda a gabana an bashi kudin amma yana kuka saboda ya yi asara,” in ji shi.

Wani ɗan ƙwadago a jihar ya ce, “gwamnati ta biya mu albashinmu, amma saboda babu kuɗi a bankuna mun zama tamkar almajirai.

“Rayuwar hannu baka hannu ƙwarya muke yi, da yawan masu sayar da kayan yau da gobe ba su da asusun banki, masu shi kuma mutane sun musu yawa”.

Kimanin mako biyu da suka wuce ne gwamnan jihar Yoben, Alhaji Maimala Buni ya koka a madadin al`ummar jiharsa cewa akwai buƙatar babban bankin Najeriya ya tsawaita wa`adin daina amfani da tsoffon takardun kudi.

Saboda ƙananan hukumomi huɗu ne rak daga cikin 17 da ke jihar suke da bankuna, waɗanda a yanzu rahotanni ke cewa inda ake da bankunan ma sun zama babban rumbu, sai a jingina da shi a kwana da yunwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *