May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wa’adin daina amfani da tsohon kuɗi bai ƙare ba’

3 min read

Wa’adin daina amfani da tsohon kuɗi bai ƙare ba’

Babban bankin Najeriya ya tabbatar wa BBC cewa har yanzu ba a daina amfani da tsofaffin kuɗi ba a faɗin ƙasar.

Wani babban jami’i a CBN ya shaida wa BBC cewa bisa la’akari da umurnin da kotun ƙolin Najeriya ta bayar na a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin har zuwa ranar 15 ga watan Fabarairu, a domin haka CBN zai bi wannan umurnin har zuwa ranar da za a koma zama a kotun.

Jami’in ya ce a hukumance CBN bai fitar da wata sanarwa ba a kan wannan batun, amma dai bankunan kasuwanci a faɗin Najeriya ba za su daina karɓar tsofaffin kudi ba har sai bayan wa’adin da kotun kolin kasar ta bayar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta ce za ta mutunta umarnin da Kotun Kolin kasar ta bayar a kan karar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar inda kotun ta dakatar da aiwatar da wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi na naira 200 da 500 da kuma 1,000.

Gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ne suka shigar karar inda suke kalubalantar wa’adin.

Ministan Shari’a kuma babban lauyan gwamnatin Najeriyar, Abubakar Malami, ne ya ce gwamnatin za ta bi umarnin a wata hira da tashar talabijin na Arise TV mai zaman kansa a Abuja.

Rashin ‘Network’
Tun daga lokacin da aka fara shirin komawa amfani da sababbin takardun kuɗi a Najeriya mutane suka fara kokawa kan rashin ‘network’ a lokacin tura kuɗi ko kuma samun su idan an turo masu ta hanyar intanet.

Wasu lokutan akan samu jinkiri ne wurin aiwatar da sakon kudin, a wani lokacin kuma abin ma ba ya yiwuwa, saboda wasu manhajojin bankunan kasuwancin kasar ba su buɗewa.

Hakan ya jefa al’umma da dama cikin garari kasancewar babu isassun kuɗi a hannun jama’a tunda Babban Bankin Najeriya (CBN) ya janye kimanin kashi 80% na tsofaffin takardun kudin bayan sauya fasalin takardun naira 1,000, da 500 da kuma 200.

Ko mene ne sanadiyyar matsalar da ake fuskanta wurin hada-hadar kuɗin ta intanet?

Mustapha Muhammad Garba masani ne kan harkokin kuɗi ya ce “tun farko ya kamata mutane su gane cewa abu biyu ne CBN ke kokarin yi a lokaci guda ”wato sauya fasalin kuɗi (Currency redesign), da kuma aiwatar da tsarin hada-hadar kudi ba tare da amfani da kudade a hannun jama’a ba (Cashless policy).

A cewarsa kowanne daga cikin waɗannan tsare-tsare biyu na da nauye-nauyen da yake tafe da su, lamarin da ya kara matsi a kan harkar banki na kasar ta Najeriya.

Ya ce “mutane sun ɗauka kawai sauya kuɗin za a yi, wato ‘currency swap’, misali, idan ka kai N100m tsofaffi a baka N100m sababbi.”

“Amma sai CBN ya shigo da batun ‘cashless policy’, abin da ya sanya ake kayyade yawan kudin da mutum zai iya cirewa daga asusun ajiyarsa a kullum.”

Yayin da ake ci gaba da fuskantar ƙarancin takardar kudin Naira, wasu bankuna a kasar sun rufe rassansu saboda karuwar hare-hare da abokan huldarsu ke kai wa gine-ginen bankuna.

Hakan na zuwa ne bayan da rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta yi gargadin cewa wasu kungiyoyi na shirin tayar da tarzoma a jihar saboda karancin sababbin takardun naira.

Tuni dai wasu daga cikin bankunan kasar suka umarci wasu daga cikin ma’aikatansu su yi aiki daga gida, yayin da wasu bankuna a jihohin Legas da Ogun da Ondo da Edo suka rufe kofofin ressansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *