May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Lokacin Kadawa Atiku Ruwan Kuri’u Yazo – Prof Hafiz Abubakar By Nura Garba

2 min read

By Nura Garba

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar yace lokaci yazo na a kadawa mai girma Atiku Abubakar ruwan kuriu a fadin tarayyar Najeriya saboda cancantarsa da kujerar shugabancin kasa.

Farfesa Abubakar yayi wannan batu ne a lokacin da yake bayani a cikin shirin siyasa wanda gidan radiyon Vision FM ya sanya a ranar Laraba da ta gabata shi da Hajiya Naja’atu Mohammed, Dr. Akilu Indabawa da kuma Dr Auwal Anwar.

Mai girma Farfesa yace jamiyyar APC anyi mata kyakykyawan tsammanin zata ceto Nigeria daga kangin da ta shiga na tattalin arziki, cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro da ya addabi bangaren Arewa maso gabas. Yace duk da dai an samu ci gaba a wannan yankin ta bangaren tsaro, amma kasar ta samu kanta a wani yanayin mummunan tsaro daya addabi kasar ta hanyar na rashin tsaro.

Farfesa yace tabarbarewar tsaron ya shafi koina a fadin kasarnan hatta garin da shugaba Buhari yake.

Ta bangaren tattalin arziki, Farfesa yayi bayani cewa darajar kudin Nigeria tayi kasa sosai kuma farashin kayan abinci da na masarufi sunyi tashin gwauran zabin da basu tabayiba tunda aka kafa kasar. Duk waddan saboda rashin kyakyawan tsari na tattalin arizi.

Sannan yace ba\a taba samun lokacin da yan siyasa suke sace kudaden kasarnan a zahirance kamar wannan lokacin ba. Hatta wasu tsofaffin gwamnoni da aka dauresu saboda an kamasu dumu-dumu da satar kudaden al\umma, amma wannan gwamnatin ta yi musu afuwa. Yace wannan abu ya bawa yan Nigeria mamamki matuka gaske.

Professor Hafiz, wanda shine jagora na kungiyar Prof Hafiz Abubakar Support Group for Atiku/Okowa 2023 yace kungiyar tayi gangami na musamman daga fadin kananan hukumomi 44 na Kano inda matasa, mata, dattijai da masu bukata ta musamman sukaci alwashin kada kuri’u ga wazirin Adamawa, Atiku Abubakar.

Hajiya Naja’atu Mohammed, Dr. Akilu Indabawa da Dr Auwal Anwar duk sunyi kira ga ilahirin yan Nigeria dasu fito su kadawa Atiku kuri’u saboda shine zai ceto kasarnan daga halin da ta shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *