May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jami’an Tsaro Sun Cafke Manajan Darakta Na Kano Line Da Sauran ƴan Daba

1 min read

Rundunar ƴan sandan jahar Kano ta cafke mutane 3 a mazaɓar Masaƙa dake unguwar ƙofar Mazugal, da ake zargi da fasa akwati da kuma zuwa da ƴan daba

Kwamishinan ƴan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel ne ya jagorancin tawagar jami’an tsaro zuwa wuraren da aka samu hargitsi.

Kwamishinan ya ce bayan faruwar lamarin ne suka garzaya wajen , kuma jami’an tsaron sun yi nasarar kama su.

CP Gumel ya ƙara da cewa yanzu haka akwai mutane 3 a hannunsu za su ci gaba da gudanar da bincike akan su.

Lamarin ya samo asali ne da yadda ya zo tare da cewa sai ya yi zaɓe awajen alhalin kuma ba akwatinsa ba ce, kawai dan ya tada fitina.

A nan ne wasu suka fito da wuƙaƙe tare da cewa sai yayi zaɓen har suka fara kai farmaki ga mutane.

Yanzu haka dai komai ya daidai ta a wajen masu son kaɗa ƙuri’unsu sun ci gaba kamar yadda aka faro tunda safiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *