Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace zata nemi Hakkinta a Kotu sakamakon yadda aka yimata magudi azaben da ya Gabata
1 min read
Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace zata nemi Hakkinta a Kotu sakamakon yadda aka yimata magudi azaben da ya Gabata
a Wani Taron manema labarai da jam’iyyar ta Kira a Yammacin yau tayi watsi da sakamakon Zaben tare da Neman Hakkinta Agaban Alkali.
Tayi Mamakin yadda aka kwace zabe aka baiwa NNPP Duk da irin kura Kurai da aka tafka yayin Zaben.
Dr Nasiru Yusuf Gawuna Wanda Kuma shine Dan Takarar kujerar Gwamnan Jihar Kano karkashin jam’iyyar APC yace sam Basu aminta da sakamakon Zaben ba, Dan haka zasu Dauki Matakin shari’a
APC ta Kawo misali da Zaben Tudun wada da Doguwa da Kuma adamawa wadanda Dukkansu akace za asake awasu Mazabu sakamakon Hargitsi Amma abun mamaki shine yadda aka Bayyana Abba Kabir Yusuf amatsayin Wanda ya lashe Zaben Gwamnan Jihar Kano Duk da kura Kurai Dake cikin zaben