May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Duk Bashin da Ganduje ya ciwo bayan an zabe ni a matsayin Gwamna bazan biya ba – Abba Kabir Yusuf

1 min read

Zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya shawarci bankuna da masu bada bashi ko lamuni na gida da na ƙasashen ƙetare da su kauce wa bai wa Gwamnati mai barin gado bashi a wannan lokacin.

Abba ya zargi cewa gwamnati mai ci ta ciyo basussuka da dama domin gadarwa Gwamnati mai zuwa.

Mai magana da yawun zaɓaɓɓen Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai.

Yace duk wani bashi ko lamuni da gwamnati mai ci ta karba daga bayan zaɓe zuwa yau, gwamnati mai jiran gado ba za ta biya shi ba matuƙar ba’a sanar da zaɓaɓɓen gwamnan ba .

“Mun ɗauki wannan matakin ne domin shi ne buƙatar al’umma kuma za mu tsaya akan sa don kare ƙima da Haƙƙin al’ummar jihar Kano”.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa gwamnati mai jiran gado za ta bibiyi duk wasu sharuɗɗa da gwamnati mai barin gado ta bi wajen karɓo bashi daga masu bada bashi da lamuni na gida da na ƙasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *