May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Al’umma da dama sun amfana da tallafin kayan abinci wanda Kungiyar Gindin Garu Sharada ta raba a yau

1 min read

Mai unguwar Sharada Gindin Garu Alhaji Ado Sa’idu ya bukaci al’umma musamman mawadata dasu dage wajen tallafawa Marayu da zaurawa dake cikin al’umma.

Alhaji Ado ya bayyana haka ne a yayin taron Rabon tallafin kayan abinci wanda Kungiyar Gindin Garu Sharada ta gudanar a yau a unguwar ta Sharada.

Ya Kara da cewa Kungiya ta dauki tsahon shekaru 20 ana gudanar da rabon tallafin wanda ke da bukatar kara kulawar mawadata domin Cigaba da gudanar da Shirin.

Alhaji Ibrahim Ango shi ne Shugaban kungiyar ya ce makasudun kafa kungiyar shi ne tallafawa Marayu domin rage musu irin radadin rayuwa da suke ciki.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin kayan abincin sun bayyana farin cikinsu, bisa taimaka musu da Kungiyar tayi.

An raba shinkafa da taliya da sauran kayayyaki da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *