May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mun raba tallafin kayan abinci ga Marayu Sama 100 domin rage musu radadin rayuwa – Mataimakin Shugaban kungiyar Indabawa Kurmawa

1 min read

Kungiyar Tallafawa Marayu dake unguwar Indabawa kurmawa wato inda Kurma ta bukaci al’umma musamman mawadata dasu dage wajen tallafawa Marayu da marasa galihu dake cikin Al’umma.

Mataimakin Shugaban kungiyar Lawan Ibrahim Sulaiman ne ya bayyana haka a yayin taron Rabon tallafin kayan abinci wanda ya gudana a unguwar a jiya.


Ya ce an raba shinkafa da makaroni ga Marayu Sama da 100 domin rage musu radadin rayuwa da suke ciki.

Ya Kuma yi kira ga sauran al’umma dasu dage da irin wadannan ayyuka domin ganin sun rabauta da irin ladan dake cikin tallafawa Marayu.

Wasu daga cikin iyayen Marayun da suka amfana da tallafin kayan abinci sun bayyana godiyar su ga Allah bisa wannan tallafi.

Kungiyar Indabawa dai ta Cigaba tana gudanar da irin wadannan ayyuka ga Marayu a yankin wanda malamai ke Kara kira ga al’umma dasu tallafawa Marayun dake yankunansu dama Jihar Kano Baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *