May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A Ranar 13 ga watan April 2007 Allah ya yiwa fitaccen Malamin Addinin musuluncin nan Sheikh Jafar Mahmud Adam Rasuwa bayan da wasu Yan ta’ada suka kashe shi lokacin da yake jagorantar sallar Asuba a Masallacin Almuntada dake Dorayi a Jihar Kano

3 min read

An haifi marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam ne a garin Daura, a farkon shekarun 1960s.

Marigayi Ja’afar ya fara karatunsa na allo a gidansu a Daura, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini.

Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari “Koza” da ke Arewa da Daura a jihar Katsina.

Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami a 1971 sai ya zauna a makarantar Malam Abdullahi a cikin Fagge. Dama can Sheikh Ja’afar ya riga ya fara haddar Alkur’ani maigirma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.

Bayan da Malamin ya haddace Alkur’ani ne sai ya ga bukatar ya samu ilmin Boko don haka ya fara karatun zamani a 1980.

Har wa yau, Malam Ja’afar ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al’adun kasar Misra (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar Boko ta manya watau “Adult Evening Classes.

” A 1983 ne Malamin ya kammala wadannan makarantu 2 na Boko da Arabiya, wanda daga nan ya samu shiga shiga makarantar GATC Gwale a 1984, har ya kammala a1988.

Bayan shekara guda ne ya wuce Jami’ar Musulunci ta Madina. A wannan babbar jami’ar musulunci ta Madinah ne Malamin ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur’an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993.

A wancan lokaci ne aka soma jin tafsirin sa na Al-Qur’ani a cikin Garin Maiduguri.
Bayan nan Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci ta Oundurman a kasar Sudan.

Kafin rasuwar Malamin, yayi nisa wajen karatunsa na PhD) a Jami’ar Usman Danfodio ta Sokoto. KU KARANTA: Takaitacen tarihin Marigayi Mai shari’a Mamman Nasir 2. Malaman Marigayi Jafar Mahmud Adam Kamar yadda Malamin ya fada daga cikin malamansa na ilimin addinin Musulunci, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago da ke cikin Kano.

A wajen Malam Dandago ne Marigayin ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi. Sauran Malaman sun hada da Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab.

Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma’a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami’ar Bayero ta Kano. Har yanzu wannan babban Malami na Hadisi Ahmad Ibrahim yana nan da ran sa. Daga cikin malamansa na jami’a kuma, akwai Sheikh Abdurrafi’u da Dr. Khalid Assabt da sauran su.

Karatu da darusan da Malam ya koyar a rayuwarsa Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur’ani mai girma. Ja’afar Adam ya sauke Al-Qur’ani kusan sau 2 a Masallacin Muhammad Indimi da ke cikin Garin Maiduguri a jihar Borno, a cikin shekaru barkatai.

Malam ya kuma karantar da Kitabuttauhiid na Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahab, da kuma littatafan hadisai na Umdatul Ahkaam, Arba’una Hadiith.

Sauran darusa sun hada da wani littafin tauhidi da ya fice mai suna Kashfusshubuhaat.

Haka kuma Malam ya karantar da litaffin nan na Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, da kuma Ahkaamul Janaa’iz, Siffatus Salaatun Nabiiy na Muhammad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *