May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wane hali ɗaliban Najeriya ke ciki a Sudan?

3 min read

Yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa tsakanin sojoji da dakarun rundunar RSF, a gwagwarmayar ƙwace iko, dubun dubatar fararen hula ne rikicin ya ritsa da su.

Akwai dai ɗaliban ƙasashen waje masu yawa da ke karatu a jami’oi’i daban-daban yanzu haka a Sudan.

Cikin irin waɗannan ɗalibai har da ɗumbin wasu da suka je ƙasar daga Najeriya inda suke karatu a fannonin ilmi daban-daban

Wasu ɗalibai ‘yan Najeriya sun shaida wa BBC cewa tun da safiyar Asabar suka farka da jin ƙarar harbe-harbe babu ƙaƙƙautawa a birnin Khartoum.

Faɗa ya kaure ne tsakanin dakarun sojin Sudan na ɓangaren shugaban ƙasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan da shugaban rundunar RSF ta masu kayan sarki a ƙarƙashin ikon Janar Hamdan Dagalo.

Shugaban ƙungiyar ɗaliban Najeriya da ke karatu a Jami’ar Sudan International University, ya ce sun samu kansu cikin wani hali na zaman ɗar-ɗar,

Muhammad Nura Bello ya ce a lokacin da harbe-harben suka farkar da shi ne ya duba waya ya ga saƙonni da kiraye-kiraye ana ƙoƙarin sanar da shi faɗa ya rincaɓe a cikin gari da kuma zagayensu.

Ya ce halin da suke ciki ya muni ne saboda sansanonin sojojin da ke kusa da su.

Jagoran ɗaliban ya ce yana tuntuɓar takwarorin karatunsa, don jin halin da suke ciki, kuma suna musayar bayanai da shawarwari kan abubuwan da suka kamata su yi, da kuma yanayin da ake ciki.

Da yake akwai yanayi na fargabar mutum bai saba ganin kansa cikin tashin hankali irin wannan ba, in ji Nura Bello.

Muna magana da juna, muna da zauren da muke tuntuɓar juna bayan sa’o’i ashirin da huɗu ko kafin nan, muna ƙoƙarin tattaunawa da juna kan halin da ake ciki, ya ce.’’

Ya ce a iya saninsu babu wani ɗalibi ɗan Najeriya da suka samu labari wani abu ya same su, sanadin faɗan da ya ɓarke a Sudan.

Shugaban ɗaliban ya ƙara da cewa sun yi ƙoƙarin ganin makarantunsu sun aika wa ɗalibai wasiƙun cewa kowa ya zauna a gida.

Haka kuma, Muhammad Nura ya ce: ‘’Muna tuntubar ofishin huldar jakadancin Najeriya a nan (Sudan), sun ce mu kwantar da hankulanmu idan akwai wani abu, za su neme mu, idan kuma mu daga ɓangarenmu, akwai wani abu, sun ce muna iya tuntuɓar su.’

Wata ɗaliba a Omdurman
Ita ma wata ɗaliba ‘yar Najeriya da ke karatu a birnin Omdurman, a yamma da Kogin Nilu, ta shaida wa BBC cewa suna cikin halin fargaba da rashin tabbas.

Ta ce suna zaune ne a cikin gida ba tare da sun san taƙamaimai me yake faruwa a waje ba.

“Gaskiya ba zan iya cewa ga halin da muke ciki ba, ko tagagogin gida ba ma iya budewa saboda fargaba, don kuwa babu abin da suke ji sai ƙarar harbe-harbe da tashin bama-bamai.

‘’Mukan ji sautin wucewar motoci jefi-jefi, ko kuma jiragen yaƙi suna ta shawagi a sama, da ƙarar tashin abubuwan fashewa da na bindigogi, su ne muke ji ko yaushe”, in ji ta.

Kamar dai sauran biranen Sudan, a cewar ɗalibar, an ɗauke wutar lantarki a yankuna da dama, sannan babu ruwan famfo, babu shi kuma har yanzu babu alamarsa ko kaɗan.

‘’Babbar matsalar ma, ita ce ba ma samun mu yi cajin wayoyinmu saboda yawan katsewar lantarkin, wadda muke da tsananin bukata, ta yadda za mu riƙa sanin halin da ake ciki a waje tun da muna cikin gida a kulle”, a cewar dalibar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *