May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yar Takarar Gwamna a Jam’iyyar APCn Adamawa, Sanata Aisha Binani ta shigar da wata Kara gaban wata Kotu dake Abuja, inda ta bukaci Kotun data duba halarci ko akasin haka na dakatar da Sakamakon Zaben da aka bayyana tai Nasara

1 min read

#Binani

‘Yar Takarar Gwamna a Jam’iyyar APCn Adamawa, Sanata Aisha Binani ta shigar da wata Kara gaban wata Kotu dake Abuja, inda ta bukaci Kotun data duba halarci ko akasin haka na dakatar da Sakamakon Zaben da aka bayyana tai Nasara.

Tun da farko dai Hedikwarar Hukumar Zabe INEC itace ta dakatar da Sakamakon da akace Binani tayi Nasara wanda PDP ta bayyana cewa ba a kamalla tattara Sakamakon ba amma Kwamishinan Zaben Jihar yayi Riga Malam Masallaci.

Lauyoyin Binani suna ganin cewa tunda aka bayanna ta a Matsayin wacce tai Nasara ba wanda keda hurumin sokewa ko dakatar da Nasarar sai Kotun zabe dokar da Order ta 34 rules 1a da order ta 3(1) da kuma sashi na 3(2) a, b, c sai Order ta 6 ta kotunan Tarayya wato Federal High Court (Civil Procedure Rules) 2019 da Kuma sashin Section 251 (1)q da r na kundin Tsarin Mulkin ‘Kasa harma da sashin Section 149 dana 152 na kundin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *