May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyatan hajjin bana zuwa kasa mai tsarki

1 min read

Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta ce babu wata jiha da take da damar kara kudin kujerar aikin hajjin bana.

Shugaban hukumar Alhazai na kasa Alhaji Zikrullah Hassan ne ya bayyana haka a wajen taron shugabannin hukumar Alhazai na jihohi da sauran hukumomi.

Ya ce duka hukumomin alhazai jihohin kasar nan 36 sun amince da kudin kujerar aikin hajji da hukumar ta sanar.

Ya kara da cewa hukumar ta amince cewa za a fara jigilar maniyyata ranar 21 ga watan Mayun gobe.

Zikrullah Hassan ya ce hukumar Alhazan za ta sake nazarin kujerun da ta warewa kowacce jiha tare da masu ruwa da tsaki a gobe Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *