May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana wata ga wata, APC ta gaza samar da daidaito a tsakanin ‘ya’yanta

1 min read

Da alama akwai sauran rina a kaba, kan batun nune da jam’iyyar APC tayi a wannan rana, na wadanda ta ke muradin su zama shugabannin majalisar dattijai da ta wakilai a sabuwar majalisar tarayya ta goma da za’a rantsar nan gaba kaɗan, domin kuwa guda cikin masu zawarcin kujerar, Mukthar Aliyu Betara, ya ƙaddamar da takarar neman shugabancin majalisar wakilai a yau.

A dai-dai lokacin da APC ta fidda sanarwar yin nune, a lokacin ne Betara ke gudanar da taron ƙaddamar da takarar tasa a babban birnin tarayya Abuja, wanda kuma aka hangi wasu cikin masu neman shugabancin majalisar a wajen taron, kamar irinsu Ahmed Wase, da Alasan Ado Doguwa, da wasu jiga-jigan majalisa.

Jam’iyyar APC dai ta ayyana Sanata Goodwill Akpabio, a matsayin wanda zai zama shugaban majalisar dattijai, da kuma Sanata Barau Jibrin a matsayin mataimakinsa, sai kuma Abass Tajuddeen a matsayin wanda suke muradin ya zama shugaban majalisar wakilai ta ƙasa, da kuma Ben Kalu a matsayin mataimakinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *