June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

NNPP ta zargi gwamnatin Kano da siyarwa dan gidan gwamna wasu kadarorin gwamnati

1 min read

Jam’iyyar NNPP mai jiran Gado a mulkin jihar Kano, ta zargin gwamnatin APC mai barin gado karkashin jagorancin gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da siyar da wasu kadarori mallakin gwamnatin jihar ga dan gidan gwamna ba bisa ƙa’ida ba, abinda tace ba zata lamunta ba, kuma za suyi bincike da tabbatar da hukunci da zarar sun karɓi mulki.

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin karɓar mulkin jihar Kano na jam’iyyar NNPP, Dakta Abdullahi Baffa Bichi, yayin wata ziyara da yakai Hukumar Kano State Public Procurement Bureau a yammacin wannan rana, bisa zargin cewa hukumar na cikin kadarorin gwamnati da aka siyarwa da dan gidan gwamna, bayan an kori ma’aikatan wajen, akan kuɗi kimanin Miliyan 10, dukda cewa darajar hukumar ya kai Miliyan 50, a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *