Shugaba Buhari Ya Bukaci Majalisar Dattawa Ta Amince Masa Karbo Bashin Dala Miliyan 800
3 min read
Makonni biyu bayan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ta dakatar da cire tallafin mai, har sai lokacin sabuwar gwamnati, duk da haka gwamnatin ta roƙi Majalisar Dattawa ta amince mata ciwo bashin dala miliyan 800 ɗin da za a raba wa marasa galihu su miliyan 50, domin tausaya masu halin ƙuncin tsadar rayuwar da za su afka, idan aka cire tallafin fetur a ƙarshen Yuni.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanta wasiƙar da Shugaba Buhari ya aika a jiya Laraba a zauren Majalisa, saura kwanaki 19 ya sauka daga mulki.
Shugaba Buhari ya ce za a tura wa talakawa miliyan 50 ɗan alawus ɗin dannar ƙirjin ba su haƙuri su rungumi tsadar fetur, bayan cire tallafi.
Ya ce Majalisar Zartaswa ta rattaba hannun amincewa, yanzu Majalisar Dattawa kaɗai ya ke jira.
Majalisar Tattalin Arzikin (NEC) ta dakatar da cire tallafin fetur da shirya yi kafin ƙarshen mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Kasafi da Tsare-tsare ta Ƙasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana wa manema labarai haka, bayan tashi daga taron su na ƙarshe a Fadar Shugaban Ƙasa.
Taron dai Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ne ya jagorance shi.
Zainab ta ce Majalisar Tattalin Arziki ta cimma yarjejeniyar dakatar da janye tallafin a yanzu, bisa la’akari da cewa idan aka yi haka a yanzu, lamarin ko kaɗan ba zai yi daɗi ba.
Zainab tace “Za a ci gaba da tuntuɓar gwamnonin jihohi da wakilan gwamnati mai jiran gado, domin tattauna yadda za a ɓullo wa lamarin.”
“Tun tuni ya kamata a ce an cire tallafin fetur, domin gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin ba. To sai dai kuma tilas idan za a cire tallafin, a cire ta yadda raɗaɗin tsadar fetur ba zai yi wa talakawa ciwo sosai ba. Wato a samu hanyar rage masu raɗaɗin tsadar fetur ɗin.
“Kenan ana buƙatar ci gaba da tattauna mafitar da za a bi da kuma yadda za a tsara bin mafitar, har a tallafa wa mutanen da tsadar fetur ɗin za ta fi shafa.”
Masana dai sun yi nuni da cewa wannan mataki alamomi ne daga Gwamnatin Tarayya akan tabbas marasa galihu za su ɗanɗana kuɗar tsadar rayuwa daga watan Yuni zuwa ‘illa ma sha-Allahu’, yayin da an kammala shirin janye tallafin fetur, lamarin da zai sa tsadar sa ta sa da yawan masu motocin hawa za a jingine ababen zirga-zirgar na su, saboda tsadar fetur.
Dalilin haka ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta fara kinkimo bashin Dala Miliyan 800 daga Bankin Duniya, domin ta raba wa marasa galihu ‘yar la’adar tausaya masu dangane da mawuyacin halin rayuwar da za au afka nan gaba daga watan, idan an cire tallafin fetur.
Bashin wanda babu ruwa a ciki, wato a Turance ‘World Bank Facility’, za a raba kuɗaɗen ne ta hanyar tuttura wa marasa galihu miliyan har su Miliyan 50, domin a rage masu raɗaɗin ƙuncin rayuwar da za su afka nan gaba kaɗan.
Zainab ta ce za a fara raba wa talakawa ta hanyar tuttura masu a asusun bankunan su, amma sai bayan an cire tallafin a watan Yuni tukunna.
Ta ce wannan Dala Miliyan 800 ba ita kaɗai ce za a raba masu ba, akwai sauran wani bashin ya na tafe, wannan somin-taɓi ne kawai.
Ta ce tuni akwai rajistar gidajen faƙirai, matalauta da marasa galihu har miliyan 10, waɗanda ta kintata yawan jama’ar da ke cikin lissafin ƙididdigar za su kai mutum miliyan 50. Ta ce waɗannan adadin duk sunayen su na cikin Rajistar Tattara Ƙidayar Marasa Galihu ta Ƙasa.
Zainab ta ce gwamnati a shirye ta ke ta rage wa marasa galihu raɗaɗin tsadar rayuwar da za su fuskanta nan gaba, ta wasu hanyoyi ba sai ta hanyar tura masu kuɗaɗen cefane ta asusun ajiyar su na bankuna ba.