Makarantu sama da biyar karamar hukumar Dawakin Tofa ta biyawa kudin Makarantar – Ado Tambai Kwa
1 min read
Exif_JPEG_420
Karamar hukumar Dawakin Tofa, ta bayar da tallafin karatu ga dalibai yar asalin karamar hukumar da ke karatu a manyan makarantu daban-daban.
Daliban makarantun dai sun hada da na kwalejin aikin gona ta Dambatta da kwalejin lafiya ta Hygiene da ta Bichi da kwalejin fasaha ta Kazaure da sauransu.
Da yake mika chekin kudin ga wakilan makarantun, shugaban karamar hukumar, Ado Tambai Kwa, ya ce tsawon lokaci suna bayar da tallafin karatun saboda muhimmancin da suka baiwa fannin ilimi.
Ya kuma kara da cewa suna biyan tallafin ne ta kudaden haraji da suke tarawa a matakin karamar hukuma.
Da yake jawabi a madadin wakilan makarantun, Sulaiman Bichi, daga kwalejin lafiya ta Bichi, ya bayyana irin gudunmawar da shugaban karamar hukumar ta Dawakin Tofa, Ado Tambai Kwa, ke baiwa fannin ilimi.
Shugaban karamar hukumar ya kuma ce baya ga fannin ilimi sun samarwa matasan karamar hukumar ayyukan yi a matakai daban-daban.