June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Hajji da Umrah ta ƙasa NAHCON tace ƙarin kuɗin da kamfanonin jirage suka nema ba zai sanya a nemi ƙari daga maniyyatan Najeriya ba

1 min read

Hukumar Hajji da Umrah ta ƙasa NAHCON tace ƙarin kuɗin da kamfanonin jirage suka nema ba zai sanya a nemi ƙari daga maniyyatan Najeriya ba.

Kamfanonin Air Peace, Azman, Max Air da Aero Contractors sun amince da ƙarin dala 250 akan kowacce kujera, sabida tsawaita nisan tafiyar da rikicin Sudan ya haddasa, bayan kulle shawagin jiragen sama a samaniyar ƙasar.

Shugaban hukumar na ƙasa ZikruLlah Hassan, yace wannan ƙari ba zai shafi kuɗin da alhazai suka biya da farko ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *