May 31, 2023

Gwamnatin tarayya ta amince a jinginar da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma Mallam Aminu Kano da ke Kano

1 min read
Share

Gwamnati ta amince da wannan mataki ne a taron majalisar koli da aka gudanar jiya a Abuja.

Ministan sufirin jiragen sama, Hadi Sirika, ya shaidawa BBC cewa za a jinginar da filin jirgin Abuja na shekara 20, sannan na Kano na tsawon shekara 30.

Sirika ya ce taron nasu ya kuma amince a sauyawa ma’aikatarsu suna daga ma’aikatar kula da sufirin jiragen sama zuwa ma’aikatar kula da sufirin jiragen sama da sararrin samaniya.

Ya kuma ce taron ya amince da wasu tsare-tsare da za su inganta harkokin sufirin jirage a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Copyright © All rights reserved. | Newsphere by AF themes.