May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Saminu Sani, haifaffen Dorayi Babba, Yamadawa da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano ta Najeriya, shi ne wanda ya lashe gasar fassara daga Faransaci zuwa Hausa wadda Kungiyar Masoya RFI karkashin daukar nauyin RFI Hausa ta shirya

1 min read

BAKANO YA LASHE GASAR FASSARA TA RFI HAUSA

Saminu Sani, haifaffen Dorayi Babba, Yamadawa da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano ta Najeriya, shi ne wanda ya lashe gasar fassara daga Faransaci zuwa Hausa wadda Kungiyar Masoya RFI karkashin daukar nauyin RFI Hausa ta shirya.

Ya doke mutane da dama daga sassan duniya da suka shiga wannan gasa, lamarin da ya bai wa kasashe renon Faransa mamaki matuka ganin cewa, Najeriya ba ta kai su karfi ba a bangaren harshen Faransanci.

Hatta alkalan da suka bayyana shi a matsayin gwarzon gasar, sun ce lallai ya cancanci yabo.

Akwai kyautar kudi da aka ware masa, kuma wannan gasar ita ce irinta ta farko, yayin da za a ci gaba da shirya ta duk shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *