May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sama da Marayu Zaurawa 400 ne suka amfana da tallafin kayan abinci – Usman Dalhatu

1 min read

Inwar Tallafawa Marayu Zaurawa dake unguwar Medile ta raba kayan abinci ga Marayu da Zaurawa Sama da 400 a a safiyar Lahadi.

Da yake jawabi Shugaban Kungiyar Malam Usman Dalhatu ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da manema labarai.

Ya Kara da cewa rabon tallafin hadin gwiwa ne da Kungiyar Da’awa da Kuma Nurul Yakin.

Usman Dalhatu ya Kara da cewa akwai bukatar masu hannu da shuni su taimakawa kokarin Gwamnatin na cigaba da Tallafawa marasa galihu domin rage irin matsin rayuwa da al’umma suke fuskanta.

Ya Kuma yi kira ga sabuwar Gwamnati Injiniya Abba Kabir Yusuf data Maida hankali wajen taimakawa Marayu da sauran marasa galihu.

Wasu daga cikin marayun da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin su bisa wannan taimako.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *