May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Cigaban tsaro da lafiya dana Ilimi Shi muka Sanya a gaba – Gwammaja Ina Mafita

1 min read

Exif_JPEG_420

Dagacin Saji Rano Alhaji Alhasan Saji Rano ya bukaci Al’umma da sauran hukumomi dasu dage wajen magance matsalar tsaro a unguwanni dama fadin Jihar baki daya.

Dagacin yayi wannan kira ne a yayin taron kaddamar da Sabon ofishin kula Harkokin tsaro dana lafiya wanda wata Kungiya dake unguwar Gwammaja ta gudanar mai sunan Gwammaja ina mafita ta shirya a unguwar.

Alhaji Alhasan ya Kuma ce bazasu saurarawa duk mutanan da suka Kama da ta da hankali al’umma ba.

Ya Kuma ce sun gudanar da Addu’o’i domin Allah ya kawo karshen matsalar kwacen waya wanda ke neman zama ruwan dare a jihar Kano.

Sannan ya bukaci masu hannu da shuni da dage wajen Tallafawa irin wadanan Kungiyoyi da dukkan gudunmawar data dage.

A nasa jawabin Shugaban Kungiyar ta Gwammaja Ina mafita Alhaji Tijjani Ali Dan Mai kunu ya ce makasudun taron shi ne kaddamar da Sabon Ofishinta,domin fara aiki nan take.

Ya Kuma ce kungiyar na gudanar da ayyuka masu yawa da ya hadar da tsaro da lafiya da kuma ilimi.

Tijjani ya Kuma bawa Kungiyar Yan sunturi ta vigilante da Civil Defense da Yan sanda bisa gudunmawar da suke bayarwa a yankin karamar hukumar Dala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *