May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Budaddiyar Wasika zuwa ga Zababban Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf game da makomar Bangaren lafiya a Jihar Kano

2 min read

A matsayina na Dan jarida Kuma Dan asalin jihar Kano na yi bincike sosai game da makomar Bangaren lafiya a Jihar Kano bisa irin lalata bangaren da akayi da Kuma yadda cin hanci da rashawa yayi yawa a bangaren.

Haka Kuma ana samun mutuwar jarirai Asbitocin jihar Kano a sakamakon karancin gado da Kuma yadda ake karbar kudade a hannun magidanta kafin a basu gado Wanda matukar aka rasa wannan kudi to ko shakka babu zaka tarar cewa an watsar da mara lafiyarka ko da kuwa mara lafiyar yana da bukatar kulawar Gaggawa.

Ya mai girma Gwamna akwai ma’aikatan Asbitocin da aka dauka wadanda basu chanchanta ba shima a bincika sosai za’aga Abinda nake fada haka yake.

Asbitin Murtala da Asbitin Nasarawa na daya daga cikin Asbitocin da ake karbar kudade masu yawa a hannun marasa lafiya wanda nake bukatar ayi bincike sosai za’a gane magana ta.

Bangaren karbar katin Asbiti kuwa shima marasa lafiya na bada kudi ana duba su batare da sun hau layi ba, shi kuwa wanda bashi da kudi ko bai son kowa ba yana nan a tsaye a cikin Rana batare da an bashi kulawa ba.

Asusun Ajiya na Asbitoci kuwa tun daga lokacin Corona har bayanta an kwashe kudade da sunan magani wanda idan Gwamna ya bincika zai gane abinda nake fada.

A kullum ana samun mutuwar jarirai da iyayensu musamman a Asbitin Murtala dake nan Kano.

Ya mai girma Gwamna idan an bani damar karin bayani domin fito da bayanai suke akan wannan bangare zan iya yi idan bukatar hakan ta ta taso.

Asbitocin Kano babu magani amma ana rubutawa cewa an fitar da makudan kudade wajen harkar sayan magani domin rabawa kyauta ga talakawan jihar Kano.

Da yawa daga cikin likitoci sun Bude Private Asbiti wanda idan an kawo mara lafiya Asbitin Gwamnati sai su bada shawara da a dauko wannan mara lafiya a dawo dashi wannan Asbiti domin a bashi kulawa.

Wadannan kadanne daga cikin abubuwan da nayi bincike akai a matsayina na dan Jarida a Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *