July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnonin jihohi sun goyi bayan cire tallafin man fetur a Najeriya

1 min read

Gwamnonin jihohin Najeriya sun nuna goyon bayansu ga matakin da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na cire tallafin man fetur.

Gwamnonin sun bayyana haka ne a lokacin wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasar a ranar Laraba.

Wata sanarwa da ta fito ta hannun daraktan yaɗa labarai na fadar shugaban Najeriya, Abiodun Oladunjoye, ta ce gwamnonin sun rinƙa yin jawabi ɗaya bayan ɗaya a lokacin ganawar, inda suka rinƙa yaba wa shugaban ƙasar kan matakin da ya ɗauka.

Gwamnonin waɗanda suka je fadar bisa jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq sun ce za su yi aiki tare da shugaban ƙasar wajen ganin an magance matsalolin da cire tallafin zai haifar.

Shugaba Bola Tinubu ne ya sanar da ƙarshen tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Maris, lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *