May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An Karrama Kawu Sumaila A Jami’ar Sa’adatu Rimi

1 min read

Sashen nazarin zamantakewar al’umma ta tsangayar ilimin zamantakewa na Sa’adatu Rimi University Of Education dake jihar kano karkashin jagorancin shugaban sashen Dr. Yahaya Salisu Abdullahi, inda ya mika lambar yabo ga sanannan dan siyarar nan Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila OFR, PHD. An bashi lambar girmamawar ne sakamakon aikin sa kai da yayi na koyarwa a jami’ar, da kuma kishin cigaban ilimi da yake dashi. Haka kuma ya kafa jami’a mai zaman kanta ta biyu mai suna Al-istiqama university dake karamar hukumar Sumaila.

Baya haka, Kawu Sumaila ya gudanar da lecture ga daliban Jami’ar yan level 3 Wadanda suke karantar Social Studies, inda ya koyar dasu darasin POST COLONIAL PERIOD.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *