May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kansilolin karamar hukumar Gwale na neman dakatar da Shugaban karamar hukumar Khalid Ishaq Diso kan zargin badakala

1 min read

Majalisar kansilolin karamar hukumar Gwale ta bukaci majalisar dokokin Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Khalid Ishaq Diso bisa zargin yin badakala.

Majalisar kansilolin ta kuma bukaci majalisar dokokin Kanon ta kafa kwamiti mai karfi da zai binciki zarge-zargen da suke masa don ladaftar dasu.

Zarge zargen sun hada da watsi da kudurorin da majalisar kansiloli ta gabatar da yin amfani da kudaden shiga na karamar hukuma ga bukatar kashin kai.

Cikin zarge zargen akwai tafiye tafiye ba tare da barin karamar hukuma a hannun kowa ba da yin wasarere da harkokin tsaro na karamar hukuma da rashin yin aiki da abokanan aikin sa.

Takardar korafin ta samu sahalewar kansilolin karamar hukumar ta Gwale da suka hada da Hamza Idi Sulaiman kabuga da Hamza Aliyu mandawari da Bashir Musa Abubakar Diso da Kabiru Sani Auwal Galadanci.

Sauran sune Aminu Dalha Dandago da Dahiru Bashir Baba Goron Dutse.

Majalisar dokokin Kanon ta mika korafin ga kwamitin ta na kananan hukumomi karkashin Zubairu Hamza Massu domin bibiya tare da gabatar da rahoton sa a ranar Litinin ta makon gobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *