May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kawu Sumaila ya ɗauki nauyin Karatun dalibai 100 a Kano ta Kudu

2 min read

Sanatan kano ta kudu Hon Sulaiman Abdurrahman kawu Sumaila, OFR, ya kaddamar da daukar nauyin karatun dalibai guda dari 100 yan asalin yankin Kano ta kudu a wasu kwalejojin Lafiya masu zaman kansu guda biyar dake jihar Kano da jahar Jigawa.

Daga cikin matasan da suka rabauta da wannan tagomashi na karatu kyauta a makarantun kudi na Lafiya a jihar Kano, akwai mata guda 50 da Maza guda 50, baya ga wasu mabiya Addinin Kirista Guda Hudu wadanda dukkanninsu suka futo daga yankin na Kudancin Kano.

Talla
Da yake kaddamar da daukar nauyin dalibai a dakin taro na Central Hotel, Sanata Kawu Sumaila yaja hankalin wadannan dalibai da su tsaya tsayin daka wajan amfani da damar da suka Samu wajan samun ingantaccen ilimi.

Mun shiga lungu da Sako na kananan hukumomin Kano ta kudu inda muka zabo matasa daban-daban wadanda zasu ci gajiyar rukunin farko na shirin tallafin karatu na waraka”. A cewar Kawu Sumaila

Wasu daga Cikin daliban da suka rabauta da samun wannan tagomashi na karatu kyauta sun bayyana farin Cikin su kamar haka.

Daga Cikin makarantun da Sanata Kawu ya dauki nauyin wadannan daliban gurbin karatu, Akwai Aminu Dabo College of Nursing, Da Emirates College of nursing dukan su a Nan Kano, dama wasu kwalejojin kiwon lafiya a garin dutsen jihar Jigawa, domin saukakawa daliban da suke da iyaka da jihar ta Jigawa, kamar Takai, Albasu, Ajingi da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *