May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Majalisar dokokin Kano ta dakatar da gina shaguna a guraren zaman Al’umma

1 min read

Majalisar dokokin Kano ta dakatar da gina shaguna tare da maida gidaje zuwa shagunan kasuwanci a karamar hukumar Fagge.

Wannan mataki ya biyo bayan rahoton da kwamitin wucin gadi kan sauya guraren zama zuwa na kasuwanci a Fagge ya gabatar yayin zaman majalisar a Larabar nan karkashin shugabanta Jibril Isma’il Falgore.

Da yake gabatar da rahoton nasa shugaban kwamitin dan majalisa mai wakiltar Nasarawa Yusuf Bello Aliyu, ya ce kwamitin ya bada shawarar kwace lasisin wadanda aka baiwa izinin gina shaguna da dakatar da sabbin gine-ginen da ake yi a guraren zaman mutane.

Haka zalika hukumar Knupda zata samar da ofishi ko ta rinka tura wakilai da zasu rinka bibiyar karamar hukumar ta Fagge don tabbatar da cewa anbi dokokin.

A dai zaman dan majalisa Usman Abubakar Tasi’u mai wakiltar Kiru ya gabatar da kudiri dake neman gwamnatin Kano ta samar da ruwan sha a wasu garuruwa dake karamar hukumar Kiru.

Yayin gabatar da kudirin dan majalisar ya ce rashin injinan wuta dake tunkudo ruwa daga matatar ruwa ta Kusalla na daga cikin dalilan da suka haifar da matsalar ruwan sha a karamar hukumar ta Kiru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *