May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Jihar Kano zata biyawa daliban Jami’ar Bayero kudin Registration su kimanin 7000

1 min read

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bada umarnin biyawa ɗaliban jihar Kano dake karatu a jami’ar Bayero (BUK) su kimanin dubu bakwai (7,000) kuɗin makaranta.

Matakin hakan na zuwa ne bayan karin kuɗin makaranta da jami’oin gwamnatin tarayya su ka yi, sakamakon janye tallafin Man Fetur, wanda yasa dalibai da dama cikin halin matsi da neman tallafi daga masu riƙe da kujerun mulki, da sauran bangarorin al’umma.

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan kafafen sadarwar zamani, Salisu Yahaya Hotoro, ne ya bayyana haka, cikin wani saƙo da ya wallafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *