May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum biyu sun mutu bayan ruftawar gini a Abuja

1 min read

Akalla mutum biyu sun mutu sakamakon ruftawar wani bene mai hawa biyu a unguwar Garki da ke tsakiyar birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na birnin Abuja, Abbas Idris, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce jami’an su na ci gaba da aikin ceto a wurin da lamarin ya faru.

Abbas Idris ya ce kawo yanzu an zaƙulo mutum 37 daga cikin ɓaraguzan ginin, inda mutum biyu suka mutu, aka garzaya da 35 zuwa asibiti.

Jami’an ceto daga hukumomin bayar da agajin gaggawa na FEMA, da jami’an kashe gobara da haɗin gwiwar jami’an kiyaye aukuwar haɗura ta ƙasar, FRSC na wurin da lamarin ya faru domin tabbatar da aikin ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ginin.

Kawo yanzu dai hukumomin ba su bayyana abin da ya haddasa ruftawar ginin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *