May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Miliyoyin mutane na kwana ba su ci abinci ba a Nijar – Hukumar Abinci

4 min read

Malanville, a arewacin Jamhuriyar Benin, na ɗaya daga cikin kan iyakokin ƙasa mafi hada-hada a Afirka ta Yamma.

Tireloli maƙare da kayan abinci da kayan agaji na jin ƙai da kayan masana’antu, galibi suna shiga suna fita ba tare da tangarɗa ba cikin Nijar mai maƙwabtaka, ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya.

Sai dai, a wani nazari da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi, hada-hada a yu duk ta tsaya cik.

Dogon layin dubban tireloli, ya kai tsawon kilomita 25 daga gaɓar Kogin Isa, da ya raba kan iyakar.

Direbobi na ta gararamba tsawon makonni, suna shanya tufafinsu a tsakanin manyan motocin.

Can nesa daga jami’an tsaron kan iyaka, ƙananan ‘yan kasuwa sun cika kwale-kwale da tulin kaya don tsallaka kogin da ya tumbatsa da ruwan sama.

Taruwar motoci jingim, na ɗaya daga cikin alamomin da suka fito fili na tasirin takunkuman da ƙungiyar Ecowas ta sanya wa Nijar, bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli.

Manufar rufe iyakar ita ce a matsa lamba ga shugabannin mulkin soja, su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed kan mulki.

Matakin, ya janyo hauhawar farashin kayan abinci a Nijar cikin wannan lokaci na tsakiyar damuna, sannan ya durƙusar da masana’antu.

Kuma yana barazanar haddasa ƙarancin magunguna a asibitoci kamar yadda hukumomin ba da agaji da jami’an gwamnati da ‘yan ƙasar suka ce.

“Mun kasa fahimta shin an yi garkuwa da mu ne, ko kuwa?” in ji wani direban tirela ɗan Nijar mai suna Soulemane, wanda aka datse shi da motar da ya ɗauko sukari da mai tsawon sama da kwana 20 a kan iyaka.

“Ba abinci, ba ruwa, babu inda za mu sa haƙarƙarinmu mu kwanta.”

Babu wata ƙwaƙƙwarar alama da ke nuna cewa takunkuman na shafar farin jinin sojoji masu juyin mulki.

A ranar Lahadi, dubun dubatar mutane sun hau tituna don zanga-zangar nuna goyon baya ga matakin ƙwace mulkin da sojoji suka yi, wasu daga cikinsu na riƙe da rubuce-rubucen nuna adawa da Ecowas.

Farin jinin shugabannin mulkin sojin Mali ga alama shi ma ƙaruwa ya yi, lokacin da Ecowas ta sa wa ƙasar takunkumai, bayan juyin mulkin shekara ta 2020 da kuma 2021.

Akwai kayayyakin agaji kimanin tan 6,000 daga Hukumar samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya da suka maƙale a can tsallaken iyakar Nijar, ciki har da hatsi da man girki da abinci don yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki, kamar yadda mai magana da yawun hukumar Djaounsede Madjiangar ya ce.

‘Yan ƙasar dai sun ce har yanzu akwai sauran abinci a shagunan birnin Niamey.

Sai dai farashinsu ya yi tashin gwauron zabi.

Tun bayan sanar da takunkuman, farashin shinkafa ya ƙaru da kashi 21%, yayin da dawa ta tashi zuwa sama da kashi 14%, a cewar Hukumar samar da Abinci.

Hukumar ta shigo da kayan abincin ne don sauƙaƙa matsalar yunwa, wadda tuni ta kama al’ummar Nijar, inda rikicin ‘yan ta-da-ƙayar-baya ya tursasa wa dubban ɗaruruwan mutane tsere wa gidajensu.

Mutane kimanin miliyan uku ne ke faɗi-tashin samun abin da za su kai bakin salati sau ɗaya a rana. Matsalar na iya tura ƙarin mutum miliyan bakwai cikin wannan hali, a cewar Hukumar samar da Abinci ta Duniya.

“A ƙarshe, muna iya samun mutum miliyan 10, da ba za su iya ciyar da kansu ba,” Madjiangar ya ce. “Buƙatun jin ƙan ɗan’adam suna ƙaruwa.”

Hukumar samar da abinci ta duniya da hukumar kula da ƙananan yara Unicef zuwa yanzu ba su kai ga rage yawan aikace-aikacensu ba a Nijar, amma dai sun yi gargaɗin cewa lokaci yana ƙurewa.

Katse ayyukan nasu, na iya yin mummunan tasiri a Nijar, ɗaya daga cikin ƙasashe mafi yawan mace-macen yara a duniya.

Kwantainonin kayayyakin Unicef na can a bakin iyaka sun rasa na-yi, da kuma a gaɓar tekun kwatano cikin ƙasar Benin.

Akwai kasadar kayayyakin asibiti masu buƙatar sanyi da alluran riga-kafi za su rasa ingancinsu. Waɗannan kuma sun haɗar da ruwan alluran mummunar ƙwayar cutar nan mai haddasa amai da gudawa, kamar yadda Hukumar ta bayyana wa Reuters a wani saƙon imel

A daidai lokacin da Ecowas da shugabannin mulkin soja ke ci gaba da kai ruwa-rana.

Ƙungiyar ƙasashen ta yi barazanar kutsawa da ƙarfin soja, idan tattaunawa da sauran ƙoƙarin matsin lamba ga sojoji masu mulki suka faskara.

“Waɗannan takunkumai ba a tsara su domin zama mafita ba, sai don durƙusar da mu, su kunyata mu,” a cewar jagoran juyin mulki, Janar Abdourahamane Tchiani a wani jawabi da ya gabatar ranar Asabar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *