May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar Manyan Ma’aikatan jami’o’i ta Ƙasa SSanu ta ce, zata cigaba da kula da walwalarar ‘Yan Kungiyar – BUK

1 min read

Wata Malama dake Jami’ar Yusuf Maitama Sule Dakta Maryam Nasir Aliyu ta bukaci mata dasu dage wajen ziyartar Asbiti da zarar sun ji wani sauyi a cikin su, domin kaucewa daga kamuwa da
kansar Ma-Ma.

Dakta Maryam ta bayyana haka ne a yayin taron da kungiyar Manyan Ma’aikatan jami’o’i ta Ƙasa Mata SSanu l, reshen Jami’ar Bayero ta shirya a yau.

Daktan ta Kuma ce, akwai abinci da matan ke ci wanda ke haifar musu da matsaloli.

Ta Kuma bukaci mata dasu dage wajen amfani da tuwon masarar da ba’a sirfataba, wanda ke zama daya daga cikin abinci me inganci.

Da take jawabi Coordinatan kungiyar SSanu bangaran mata reshen Jami’ar Kwamared Farida Sani Kamba ta bayyana cewa kungiyar na gudanar da ayyuka da dama musamman baiwa Yan kungiyar kayan abinci wanda ake biya da kadan -kadan.

Ta kuma Kara da cewa hatta marasa lafiya da Ma’aikatan da mazajensu suka rasu, suma kungiyar na basu tallafi da dai sauran ayyuka da kungiyar take gudanarwa.

A yayin taron dai gabatar da Makalu da dama wanda ya Sami halarta manyan Ma’aikata mata da maza yayin da wasu suka zo daga arewacin Kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *