May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Kano ta rage kashi 50 na kudin rijista ga daliban manyan makarantun jihar

2 min read

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta rage wa daliban manyan makarantun jihar kudin makaranta da kashi 50 cikin 100.

Gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan a shafukansa na sa da zumunta a daren Litinin.

Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ya karbi bakuncin shugabannin makarantun gaba da sakandire mallakin gwamnatin jihar.

Abba Kabir, ya ce ya ba da umarnin rage kudin makaratar nan take.

Hakan dai na nufin daga yanzu daliban Kano da suke karatu a makarantun gaba da sakandare mallakin gwamnatin jihar za su rinka biyan rabin kudin da suke biya ne.

Kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya shaida wa BBC cewa, gwamnatin jihar ta duba yanayin kuncin rayuwa da ake ciki wanda abin ya ta’azara bayan janye tallafin man fetir.

Ya ce, a yanzu abubuwa sun kara tsada kamar kudin mota da kayan abinci da ma sauran abubuwan da ake ta’ammali da su na yau da kullum.

Kwamishinan ya ce, ” A duk lokacin da aka samu yanayi na tsadar kayan abinci, to iyaye kan sha wuya wajen biyawa ‘ya’yansu kudin makaranta, to wannan dalilin ne ya sa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce bari a nemi hanyoyin saukakawa iyaye da ma dalibai a wannan hali da ake ciki shi ya sa ma ya ce bari abi dukkan manyan makarantu mallakin gwamnatin jihar su takwas a rage kudinsu ta yadda iyayen yara da adlibai za su biya rabi gwamnati ta cire sauran rabin”

Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya ce an dauki wannan mataki ne don a tallafawa ilimi da farfado da shi, sannan kuma ya zama wani tallafi a wannan shekarar wajen rage radadin rayuwar ma da ake ciki.

Kwamishinan ya ce sun shirya tsaf don ganin komai ya tafi daidai a wannan tsari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *