May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Siyasar Kano: APC da NNPP sun koma ga Allah kafin hukuncin kotu

3 min read

Hausawa kan ce komai ya yi zafi, maganinsa Allah!

Ga dukkan alamu, manyan jam’iyyun Kano biyu, sun mayar da al’amarin nasu ga Allah, daidai lokacin da suke jira kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar ta sanar da hukuncin da ta yanke a nan gaba.

Hukuncin kotun dai yana da matuƙar muhimmanci ga jam’iyyun NNPP mai mulki a ƙarƙashin jagorancin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da APC mai adawa wadda Dr. Abdullahi Umar Ganduje ke jagoranta.

Kwankwaso da Ganduje dai, manyan aminan juna ne da suka yi siyasar ubangida da yaronsa a jihar, kafin su rikiɗe su koma manyan abokan adawar juna.

Magoyan bayan jam’iyyar APC mai adawa a Kano, suna ci gaba da tarukan addu’o’i da saukar Alƙur’ani a mazaɓu da ƙananan hukumomi, bayan da yawansu sun yi azumin nafila a ranar Litinin.

Matakin na zuwa ne bayan tun da farko, ‘ya’yan jam’iyyar NNPP mai mulkin Kano sun gudanar da irin wannan taron addu’o’i, bayan gudanar da sallah a ranakun ƙarshen makon da ya gabata.

Ɗaruruwan magoya bayan NNPP ne suka taru a filin wasa na Ƙofar Na’isa sanye da jajayen huluna ranar Asabar don gudanar da salloli da kuma addu’o’un neman nasara.

Su ma gomman magoyan APC sun gudanar da saukar Ƙur’ani a Masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani da ke Ƙofar Mata da kuma addu’o’i a ranar Lahadi.

Haka nan, magoya bayan Nasiru Gawuna na APC sun yi wani taron a mazaɓarsa ta Gawuna da ke cikin ƙaramar hukumar Nassarawa, inda suka yanka dabbobi.

Yunƙurin nasu na zuwa ne yayin da ake jiran hukuncin da kotun za ta yanke a ƙarar da APC da ɗan takararta Nasiru Yusuf Gawuna suka shigar don ƙalubalantar nasarar gwamna mai-ci Abba Kabir Yusuf da NNPP.

Siyasar Kano ta ƙara zafi ne bayan alƙaliyar kotun, Mai Shari’a Flora Ngozi Azinge, ta yi zargin cewa ana yunƙurin ba su cin hanci da zimmar sauya hukunci. Sai dai ba ta faɗi jam’iyya ko mutanen da take zargi ba.

Hukumar zaɓen Najeriya, Inec, ta ayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris bayan ya samu ƙuri’a 1,019,602, sai kuma Nasiru Gawuna na APC – mai mulkin jihar a lokacin – da ya zo na biyu da ƙuri’a 890,705.

Wannan ne karo na uku da jam’iyyar adawa ke doke mai mulki a jihar Kano cikin shekara 24 – bayan komawa mulkin dimokraɗiyya a 1999 – don kuwa, an yi hakan a 2003, da 2011.

‘Wanda ma yake zalunci ya yi addu’a ballantana wanda aka zalunta[?]’

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ce ke riƙe da madafun iko lokacin da NNPP ta doke ta a zaɓen na watan Maris, wanda hakan ya sa take zargin ‘yan adawar da yin maguɗi da kuam “zalinci”.

APC ta ce ta lura da yadda ‘yan NNPP suka rungumi addu’o’i “duk da cewa su ne azzaluman”, shi ya sa ita ma ta umarci ‘ya’yanta su koma ga Allah.

“Sai muka ga wanda ma yake zalinci ya hyi addu’a ballantana wanda aka zalinta, shi ya sa muka yanke hukuncin fawwala wa Allah, mu kai kuka gare shi don ya share mana hawaye,” kamar yadda Sakataren APC na Kano Abdullahi Sarina ya shaida wa BBC.

Sai dai ya ce rungumar addu’o’in ba ya nufin “gazawa”, yana mai cewa “shari’a mace ce da ciki, ba a san abin da za ta haifa ba.

“Duk wanda ya shiga shari’a kuma yake cewa yana da tabbas zai yi ci [nasara], to bai san mece ce shari’a ba. Duk abin da aka ce gaibu ne, to sai a bar wa Allah hukuncinsa.”

Jagororin jam’iyyar sun umarci magoya bayansu a faɗin Kano baki ɗaya su ci gaba da yin azumin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *