May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Babu wanda ya isa ya kori Kwankwaso daga NNPP – Buba GaladimaQ

2 min read

Wani tsagin na jam’iyyar NNPP mai mubaya’a ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da korar ƴan kwamitin amintattun da suka dakatar da jagoran jam’iyyar.

Ɗaya daga cikin jigo a jam’iyyar da ke biyayya ga Kwankwaso, Injiniya Buba Galadima ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne a wani taro da suka gudanar a Abuja a wani yunkurin na fasalta al’amuran jam’iyyar.

Wannan mataki na zuwa ne bayan a ranar Talata an samu labarin da ke cewa NNPP ta dakatar da Kwankwaso kan zargin yi wa jam’iyyar zangon-kasa.

Sai dai Injiniya Galadima ya ce sun yi mamakin jin labarin dakatar da Kwankwaso saboda su ne kwamitin amintattun, kuma ba su san da zaman ressan jam’iyyar da ke cewa sun dakatar da Kwankwaso ba.

Ya ce akwai lokacin da suka kaddamar da kwamitin bincike kan waɗanda suka aikata laifuka a jam’iyyar kuma shi a iyakar saninsa babu Kwankwaso a ciki.

Duk da, a cewar Buba Galadima, Kwankwaso bai fi karfin bincike ba idan akwai zargi a kansa.

Sannan Buba Galadima ya ce su wadanda suka yi sanarwar dakatar da Kwankwaso sun yi hakan ne bayan samun labarin za a kore su daga jam’iyyar.

Kuma ya shaida cewa babu wani lokaci da Kwankwaso ya gana da ɓangaren APC ko shugaban kasa ba tare da ya tattaunawa da uwar jami’iyyar ta NNPP ba.

Wata ƙungiya ce a ƙarƙashin jagorancin wasu ƙusoshin NNPP, Mista Boniface Aniebonam da Agbo Major suka bayyana matakin dakatar da Kwankwaso bayan wani babban taro na musamman a birnin Ikko cikin jihar Lagos.

Haka zalika sun sanar da dakatar da kwamitin zartarwar NNPP na ƙasa.

Rahotanni sun ce ƙungiyar na cewa “ƙwararan shaidu” da suka bayyana sun tabbatar da cewa Kwankwaso na da hannu dumu-dumu a “wasu harkoki na yi wa jam’iyyar zagon ƙasa yayin taruka daban-daban”.

Kuma sun zargi Kwankwaso da yin tattaunawar siyasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tun lokacin yana ɗan takara a jam’iyyar APC da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi.

Sun ce matakin dakatarwar ya zo bayan binciken da wani kwamitin ladabtarwa ya yi.

Sai dai, ɓangaren Kwankwaso ya ce mutanen da suka yi dakatarwa tuni da ma an riga an kore su daga jam’iyyar NNPP.

Kwankwaso dai shi ne ya zo na huɗu a zaɓen shugaban ƙasan da ya gabata, inda ya samu ƙuri’a 1,496,687.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *