May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutanen gari sun yi garkuwa da iyalan ‘yan bindiga a Zamfara

2 min read

A Najeriya, batun matsalar tsaro ya dauki sabon salo, sakamakon yadda jama’ar gari suka fara mayar da martani, ta hanyar cafke da kuma yin garkuwa da iyalan ‘yan bindiga.

Har wasu matasan yankin Birnin Magaji na jihar Zamfara sun yi garkuwa da wasu matan aure na ‘yan bindiga, ciki har da wata mai juna biyu.

Matasan sun yi ikirarin cewa sun dauki wannan mataki ne bayan da ‘yan bindigan suka sace mutanen yankin su bakwai da ababen hawansu.

Matasan sun ce ba za su saki matan ‘yan bindigan da suka damke, suke garkuwa da su ba, har sai mazansu sun sako wasu mutanen yankin da suka sace a baya baya nan.

Wani mutumin yankin da abin ya auku, wanda ya gwammace a sakaya sunansa, ya yi karin bayani kan wannan dakasarama:

“Ana ta juyayi sai ga wadannan matan ‘yan bindiga sun zo, sai mutane suka ce ba za su wuce ba kuma ba za su sakesu ba sai an kawo ‘yan uwanmu da aka kama,” in ji shi.

Mazaunin yankin ya ce ‘yan bindigar sun kira matan nasu ta waya inda suka nemisu da su yi kokari a sakesu don suna cikin ‘mawuyacin hali‘.

Matashin ya kuma musanta zargin da ake yi kan cewa mazauna yankin sun dauki doka a hannunsu:

“Wannan an riga an dange mu ne, mun rasa yadda za mu yi da rayuwarmu, ka fita daji ba dadi, ka dawo gida ba dadi, ka yi kwance ba dadi.

Rahotanni sun ce a gona ‘yan bindigan suka sace mutanen na Birnin Magaji, a cewar wani mutumin yankin, wanda shi ma ba ya so a fadi sunansa:

“Su na gona wurin aiki, sai ga wadanan ‘yan bindiga su kusan goma sha,suka zagayesu da bindigogi, to da suka ga sun fi karfinsu sai suka bada hadin kai aka tafi da su “ in ji shi.

Yan bindigar sun sace mutun 7 da farko amma daga bisani daga cikinsu ya dawo gida.

Mutanen da suke garkuwa dasu sun hada da maza 4 da mata 2.

Kallo a yanzu ya koma ne kan yadda wannan ja-in-ja za ta kaya, tsakanin matasa da ’yan bindiga a yankin na Birnin Magaji a jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *