May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa za ta yanke hukunci kan shari’ar zaɓen da ke tsakanin Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar LP, da Shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC

1 min read

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa za ta yanke hukunci kan shari’ar zaɓen da ke tsakanin Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar LP, da Shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.

Kotun zaɓen za ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba da muke ciki kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Tun bayan sanar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe ne dai Atiku da Peter Obi ke ƙalubalantarsa a gaban kotu, su na iƙirarin cewa bai cancanta ba, kuma zaɓen na sa da aka yi wanda ya kai ga ba shi nasarar zamowa shugaban ƙasa cike yake da kura-kurai.

Ana sa ran cewa kotunan zaɓen da ke a jihohin Nigeria daban-daban, za su sanar da hukunce-hukuncen shari’o’in zaɓuƙan gwamna da suka gudana a jihohi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *