May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yan sanda sun fara dirar mikiya kan masu yaɗa jita-jitar ‘matsafa masu shan jini’

2 min read

Sakamakon jita-jitar da ta gauraye wasu sassan arewacin Najeriya game da wasu mutane da ake zargin masu shanye jini da ‘yan shafi mu-lera, ‘yan sanda sun fara yin dirar mikiya a kan wasu da ake zargin suna yaɗa irin wannan jita-jita, da kan janyo a far wa wasu mutane da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ana ta yaɗa jita-jitar cewa wasu mata na yin sallama a gidajen mutane, inda suke roƙon ruwan sha, amma a cewar masu jita-jitar sai mutanen su zuƙe wa wanda ko wadda ta ba su ruwa jini.

A wata ruwayar kuma, an ce mutanen da ake zargi suna kwashe wa namiji mazakuta, yayin da mace take rasa mamanta.

Irin wannan jita-jita dai, ta kai ga har cincirindon mutane suna far wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a jihohi kamar Kano da Bauchi da Kaduna.

Sai dai a yanzu, hukumomi sun fara yin dirar mikiya a kan mutanen da ke yaɗa irin wannan jita-jita maras tushe.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fitar, ta ce wannan lamari ya yi ƙamari ne tsakanin ranar Juma’a zuwa ranar Lahadi 3 ga watan Satumba.

Ta yi Allah-wadai da abin da ta kira “cin mutuncin matafiya da baƙin fuska” a unguwannin da ba a san su ba.

Inda ta ce ta gudanar da bincike kan wasu daga cikin koken da aka shigar mata kuma ta gano duka zarge-zarge “ba su da tushe, balle makama, don haka, ƙarya ne”.

Sanarwar da kakakin rundunar a Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce ” wasu ɓata gari ne ke neman ta da zaune-tsaye ta hanyar haifar da gaba da ƙiyayya da jefa tsoro da firgici a zukatan mutane domin hana zaman lafiya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *