May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ƙungiyar ‘yan ƙwadago ta fara yajin aikin gargaɗi na kwana biyu

2 min read

Yajin aikin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ga alama ya kankama a wasu sassa na ƙasar, inda ma’aikata da yawa suka ƙauracewa wuraren aiki ciki har da bankunan kasuwanci.

Ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwana biyu ne don nuna fushinta a kan rashin cimma matsaya da gwamnati game da matsin rayuwa da mawuyacin hali da al’ummar ƙasar suka shiga bayan janye tallafin man fetur.

A makon jiya, NLC ta ce za ta gudanar da yajin aikin kwana biyu a matsayin gargaɗi ga hukumomin Najeriya don su san halin da ‘yan ƙasar ke ciki.

Wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Joe Ajaeru ya fitar, ta ce yajin aikin ya zama dole, saboda gwamnatin ƙasar ba ta mutunta yarjejeniyar da suka cimma ba.

Ya ƙara da cewa gwamnati ba ta damu da halin da ‘yan Najeriya ke ciki ba game da wahalhalu saboda cire tallafin man fetur.

Sanarwa ta ce NLC ta fara da yajin aikin kwana biyu ne don nuna wa gwamnati cewa a shirye suke su shiga wani yaji na tsawon mako biyu ko uku nan gaba a faɗin ƙasar.

“Za mu shiga yajin aikin baki ɗaya domin durƙusar da ayyuka a faɗin ƙasa na kwana 14 ko 21 har sai an ɗauki matakin da ya dace na ceto mutane daga wahalar da suke fama da ita,” in ji sanarwar.

Za kuma a yi “zanga-zanga a jihar Imo a wannan watan na Satumba” domin tursasa wa gwamnati ta sauya manufar ƙasƙantar da ma’aikata.

Kwanan baya, ƙungiyar ta gudanar da zanga-zangar share fagen shiga yajin aiki, amma daga bisani sai ta cimma matsaya da gwamnati bayan wata ganawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A Kano, rahotanni sun ce bankuna da yawa ba su buɗe ba saboda yajin aikin ‘yan ƙwadago na ranar Talata.

Haka zalika, an ga shugabannin ƙungiyar NLC a Kano a lokacin da suka je ofishin hukumar raba lantarki a jihar Kedco, inda suka rufe shi, a kan titin Post Office. Sun ce matakin, yunƙuri ne na ganin duk ma’aikata sun shiga wannan yajin aiki da uwar ƙungiyar ta ba da umarni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *