May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum 12 sun mutu a haɗarin mota a Kogi’

1 min read

Hukumar kare haɗɗura ta Najeriya ta ce akalla mutum 12 ne suka mutu a wani mummuna haɗari ranar Lahadi a kan titin Obajana-Lokoja a jihar Kogi.

Jami’in wayar da kan al’umma ACM bisi Kazeem ya tabbatar da mutuwar mutane cikin wata sanarwa da ya fitar wadda kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya wallafa.

Kazeem ya kuma ce akwai mutum shida cikin motar da suka ji munanan raunuka.

Ya ƙara da cewa haɗarin ya rutsa da wata mota ne ƙirar Toyota Hiace mai lamba MKA515ZD da wata gingimari.

Ya ce duka mutane 18 da ke cikin motar hayar maza ne.

Ya kuma shawarci matuƙa da su riƙa kiyaye yanayin gudunsu wanda hakan zai taimaka wajen rage yawan haɗura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *