May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta tabbatar da nasarar zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu

3 min read

Shugaban kotun, Mai shari’a Haruna Tsammani ya ce matakin hukumar zaɓe na ayyana Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen 25 ga watan Fabrairu, ya dace.

Matakin na zuwa ne bayan kotun ta kori ƙarar ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar adawar Najeriya, Atiku Abubakar da maryacen Laraba.

Shi, da Peter Obi na jam’iyyar Labour da kuma jam’iyyar APM, sun nemi kotun ta soke nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen Fabrairu.

Sai dai, ba a ga ‘yan adawa irinsu Atiku da Peter Obi a zaman kotun na ranar Laraba ba, yayin da manyan jami’an gwamnati ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje suka shafe tsawon wuni suna sauraron hukuncin kotun.

Da farko, kotun ta yi watsi da ƙarar Peter Obi na jam’iyyar LP da ta jam’iyyar APM.

Ta kuma ce duk ƙararrakin, waɗanda aka shigar don neman a soke cancantar zaɓen Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, ba su da tushe.

Alƙalan kotun biyar wajen gabatar da hukuncin, wanda suka shafe tsawon wunin ranar Laraba, suna gabatarwa.

Sun riƙa karɓa-karɓa wajen yin bita da karanta hujjoji, tare da tsefe bayanai, kafin bayyana matsayarsu a kan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar.

Tuni fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwa, inda ta ce Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin kotun cike da tsananin sanin nauyin da ke kansa, da kuma shirin hidimtawa dukkan al’ummar Najeriya.

Shugaban na Najeriya ya kuma bai wa al’ummar Najeriya tabbacin mayar da hankali wajen cika ƙudurinsa na samar da ƙasa mai haɗin kai da zaman lafiya da bunƙasar arziƙi.

Tinubu ya kuma ce ya yaba wa tsayin daka da jajircewar bin diddigin komai da kuma ƙwarewa daga alƙalan kotun biyar a ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsammani ga fashin baƙin doka.

Tinubu ya ce ya yi imani cewa ‘yan takarar shugaban ƙasa da jam’iyyun siyasar da suka yi amfani da ‘yancin da doka ta ba su dama wajen shiga babban zaɓen da kuma bin tafarkin zuwa kotu, sun tabbatar da matsayin bin tafarkin dimokraɗiyyar Najeriya.

Ya kuma buƙaci su zaburar da magoya bayansu wajen yin amanna da aƙidar kishin ƙasa, ta hanyar mara wa gwamnatinsa baya don bunƙasa rayuwar duk ‘yan Najeriya.

Atiku bai gabatar da shaidun da suka dace ba – Kotu
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen dai ta yi watsi da ƙorafin Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP da neman a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihohin Kano da Lagos.

Ta ce masu ƙorafin ba su shigar da Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso ba a ƙararsu, duk da yake su ne suka ci mafi rinjayen ƙuri’un da aka kaɗa a jihohin biyu.

Haka kuma ta kori bahasin ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar wanda ya zargi Bola Tinubu da mallakar takardun shaidar ɗan ƙasa biyu wato Najeriya da ƙasar Guinea

Sannan ta yi watsi da iƙirarin cewa kotu ta taɓa kama Tinubu da laifin safarar ƙwaya a Amurka.

Ma shari’a Tsammani ya buga misali da shaidar da ayarin lauyoyin Tinubu ya gabatar na wata wasiƙa daga ofishin jakadancin Amurka da ke tabbatar da rashin tarihin aikata laifi na Tinubu a Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *