May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Majalisar Wakilan Najeriya za ta fara bincike kan ɓarayin ɗanyen mai a ƙasar

1 min read

Wani kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya da ke bincike kan satar ɗanyen mai da ake yi da kuma asarar kuɗin shiga da ake samu na gas ya yi alƙawarin bayyana sunayen mutanen da ka da hannu cikin lamari.

Ɗan Majalisa Kabiru Rurum wanda shi ne shugaban kwamitin ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nan gabanin fara sauraren binciken ranar 7 ga watan Satumba.

Ya ce ɓangaren mai shi ne babbar hanyar da Najeriya ke samun kuɗin shiga, inda ya ƙara da alƙawarin cewa wannan binciken zai sha ban-ban da na baya da aka yi.

A cewarsa, ɓanagern mai da gas sune manyan abubuwan da ƙasa ta dogara a kansu, amma matsalar satar mai na ci gaba da ƙazanta a Najeriya a kullum.

“Dalilin wannan kwamitin shi ne ya bankaɗo sunan mutanen da ke da hannu cikin wannan satar da ake yi ta ɗanyen mai.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *