May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin jihar Kano ta ce za’a dawo da ƙarɓar Harajin kullum-kullum na matuƙa Baburan Adaidaita Sahu a faɗin jihar nan

1 min read

Kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano Engr. Muhammad Diggol ne ya bayyana haka a yammacin jiya Juma’a a helkwatartar Hukumar KAROTA.

Lokacin da yake ganawa da Ƙungiyoyin sufurin Adaidaita Sahu na jihar nan, ya ce ya zama wajibi Gwamnati ta ci gaba da karbar harajin ga matuƙa Adaidai Sahu domin ciyar da jihar Kano ta ɓangaren sufuri gaba.

Kwamishinan ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za’a sabunta rijistar Adaidaita Sahu domin tantance matuƙan, tare da sanin adadinsu a faɗin jihar Kano

Yace za’a ɓullo da sabbin tsare-tsare waɗanda za su sauƙaƙawa matuƙan biyan harajin kullum-kullum tare da sabunta rijistar ba tare da an musguna musu ba, duba da yanayin da ake ciki na matsayin rayuwa.

Ya ce ya zama wajibi Gwamnati ta san mutanen da suke tuƙa Adaidai Sahun duba da yanayin da ake ciki. A don haka ko wanne matuƙi dole ne sai ya samu shaidar sa hannu daga Mai Unguwarsa kafin a yi masa rijistar, hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a fadin jihar nan baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *