May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ma’aikatar ilimi ta Kano ta amince da Ranar 10 ga wata a matsayin Ranar komawa Makaranta

1 min read

Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta amince da ranar Lahadi 10 ga Satumba, 2023 a matsayin ranar da za’a koma makarantun kwana na gwamnati da na firamare masu zaman kansu da na gaba da firamare a jihar don fara karatun zangon farko na shekarar 2023/2024.

Hakazalika, Dalibai a makarantun jeka ka dawo za su koma ranar Litinin 11 ga Satumba 2023.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Balarabe Abdullahi Kiru, ta ce ma’aikatar ta umarci Iyaye da su lura da ranar da aka kayyade komawa aiki domin tabbatar da bin ka’ida.

An kuma gargadi cewa za’a dau matakin ladabtarwa akan duk Dalibin da bai koma ba a Ranar da aka sanar.

Har ila yau, kwamishinan ilimi na jihar Umar Haruna Doguwa ya bayyana kudirin gwamnati mai ci na inganta jin dadin malamai, inda ya bayyana cewa gwamnan ya kafa wani kwamiti da zai magance matsalolin da suka shafi kara wa malamai da sauran hakkokinsu don inganta yanayin aikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *