May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ba ma goyon bayan shirin gwamnati na bai wa jami’o’i cin gashin-kai – ASUU

2 min read

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU ta ce ba za ta goyi bayan shirin gwamnatin tarayyar ƙasar na bai wa jami`o`i da manyan makarantu `yancin cin gashin-kai ba.

A wannan makon ne Ministan Ilimin ƙasar Farfesa Tahir Mamman, ya ce gwamnatin tarayyar na shirin fito da wasu sabbin hanyoyi ta yadda jami’o’i da manyan makarantun gwamnati za su dinga cin gashin kansu.

Ƙungiyar malaman jami’o’in ta ce irin cin gashin-kan da gwamnatin tarayyar ke tunani ba zai kasance alheri ba ga ‘yan Najeriya.

A tattaunawarsa da BBC, shugaban shiyyar Kano ta ƙungiyar, Farfesa Abdulkadir Muhammad, ya ce, abin da gwamnatin take son yi a yanzu ya saɓa da wanda suke hanƙoron a yi.

Ya ƙara da cewa, matakin na nuna cewa gwamnati tana son ta kauce daga nauyin da ta ɗora wa kanta ne domin a cewarsa jami’o’in ai na gwamnatin tarayya ne ba na wani ba.

‘Matakin ba shi da alaƙa da tsarinmu’
To amma ganin cewa bayar da ‘yancin cin gashin-kai ga jami’o’in gwamnatin tarayyar abu ne da ASUU ta daɗe tana nema sai kuma yanzu ga shi gwamnatin tana son yin hakan sai malamin ya ce wannan ba irin tsarin da suke fafutuka a kai ba ne.

Ya ce : ‘’Yancin da muke magana a kai ba shi suke magana ba.’’

Abin da ƙungiyar ASUU take buƙata shi ne misali gwamnati ta tsame kanta a kan yadda ake zaɓen shugabanni da yin dokokin da suke ganin ba su dace da tafiyar da jami’a ba.

Farfesan ya kuma bayar da ƙarin misali kan yadda ya ce gwamnati za ta kawo wasu dokoki da suka shafi sauran ma’aikata a ce za a yi amfani da su a kan malamai ko ma’aikatan jami’o’i.

A nan malamin ya bayar da misalin tsarin biyan albashi na IPPIS, inda ya ce wata kotu a ƙasar ta yi hukunci da cewa bai dace a yi amfani da wannan manhaja a tsarin jami’o’i ba.

Ya ce, ” amma a maganar bayar da kuɗaɗen tafiyar da jami’a, gwamnati ta ce ba za ta bayar ba, to wane ne zai bayar tun da jami’o’in nata ne mallakarta to matsalar ita ce wane ne zai bayar da kudaden?’’

‘’Idan aka ce jami’o’i su za su nemo kuɗin da za su tafiyar da kansu to ana gaya wa mutane ke nan cewa su shirya, ‘ya’yansu ko kuma su za su nemo waɗannan kuɗaɗe,’’ in ji malamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *