May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mun kawo ƙashen dokar zaman gida a kudu maso gabas – COAS

1 min read

Babban hafsan sojin sama na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana cewa matakin da tsageru ke ɗauka na tursasa mutane zaman gida a yankin kudu maso gabacin Najeriya ya zo ƙarshe.

Janar Lagbaja ya bayyana hakan ne ranar Talata a lokacin wani taro da yaka shiraya na watannin rubu’i na biyu da na uku na wannan shekara.

Ya bayyana cewa an samu nasarar kawar da batun zaman gidan ne sanadiyyar hoɓɓasa na dakarun Najeriya tare da na masu ruwa da tsaki.

Ya ce “a yanzu al’umma masu bin doka na gudanar da lamurransu a kodayaushe ba tare da tarnaƙi ba.”

Ya ƙara da cewa “mun ƙara ƙaimi a ƙoƙarinmu na kawar da ayyukan assha da ƙungiyar IPOB da ESN ke tafkawa a kudu maso gabashin Najeriya. Ta hanyar shrinmu na ‘Operation Udoka’ jami’anmu da sauran masu ruwa da tsaki sun kawo ƙarshen dokar zaman gida da ta kusa kassara tattalin arziƙin yankin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *