Abba El Mustapha na fuskantar ƙalubale a masana’antar fim
1 min read
Tun bayan fitar da sanarwar soke lasisin jarumai a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood tare da sabunta lasisin da hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano, karkashin jagorancin Abba El Mustapha (Abba Na Abba), tayi a baya bayan nan, lamarin ya haifar da cece-kuce a tsakanin jarumai da masu bada umarni a masana’antar.
Sunusi Oscar 442, mai bada umarni yace babu sanin ya kamata akan lamarin, kuma da ace anyi shawara dashi da bazai bari ayi haka ba, kana kuma yace tunda aka bawa Abba El Mustapha shugabancin hukumar, suka fuskanci ya janyo maƙiyan Gwamnatin Kano jikinsa, wanda yin hakan kamar Ungulu ce da kan Zabo.
Shima a nasa bangaren, jarumi Mustapha Badamasi Naburaska, ya soki tsarin, inda yace ba a yanzu ya kamata a fito wannan tsari ba, domin mafi yawan jarumai basu da ƙarfin tattalin arzikin da zasu sabunta lasisi a yanzu, harma yace gwamnatin Kano za ta iya fita daga ransa akan wannan abu.
Sai dai kuma, tuni jarumai irinsu Ali Nuhu, Sani Danja, Yakubu Muhammad da sauransu, suka ziyarci hukumar su ka sabunta lasisin nasu, harma su kayi kira ga sauran abokan sana’arsu da su yi ƙoƙari su sabunta lasisin su.
#