An samu musayar kalamai tsakanin yan Kwankwasiyya sa Salihu Tanko Yakasai
1 min read
Musayar kalamai ta barke tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya da tsohon dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PRP a babban zaɓen shekarar 2023, Salihu Tanko Yakasai, kan batun shari’ar zaɓen gwamnan Kano, bayan wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook da yake nuna kotu zata karɓi kujerar gwamnan Kano daga hannun Injiniya Abba Kabir Yusuf ta miƙawa Nasiru Yusuf Gawuna.
Yakasai wanda ya samu ƙuri’u 2,183 a sakamakon zaɓen gwamnan Kano da ya gabata karkashin jam’iyyar PRP, ya sake komawa APC a baya bayan nan, domin ya bawa shugaban riƙon jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gudummawa a sha’anin gudanarwar jam’iyyar APC.