September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar lauyoyi ta yabawa Abba Kabir Yusuf bisa daukar matakin nan take

1 min read

Ƙungiyar lauyoyi ta jinjinawa gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa sauke jami’an gwamnatinsa guda biyu daga muƙamansu, kan kausasa harshe da su kayi akan Alƙalai kan batun shari’ar zaɓen gwamnan Kano, da kuma mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

Shugaban ƙungiyar reshen jihar Kano, Barista Sulaiman Gezawa, ne ya bayyana haka, inda yayi kira ga jami’an tsaro da su gudanar da bincike akan wadanda ake zargi da furta kalaman.

A ranar Juma’a ne gwamnan Kano ya cire kwamishinan ma’aikatar harkokin ƙasa da safayo, Adamu Aliyu Kibiya, da mai bashi shawara akan harkokin matasa da wasanni, Ambasada Yusuf Imam, daga muƙamansu bisa furta kalamai na barazana ga Alƙalan kotun zaɓe da kuma furucin da bai dace ba ga mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, inda gwamnan ta hannun kwamishinan yaɗa labarai, Baba Halilu Dantiye, yace sun furta kalaman ne bisa radin kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *