September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Cibiyar tsaron Najeriya za ta yi bincike kan ‘bidiyon ƴan bindiga a Katsina

2 min read

Cibiyar tsaron Najeirya ta ce ta kaddamar da bincike kan wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta da ke nuna wasu da ake zargin sojoji ne suna magana da wasu mutane a kan babura ɗauke da makamai, waɗanda ake tunanin ƴan bindiga ne.

Ana zargin cewa an ɗauki bidiyon ne a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

A cikin faifan bidiyon an ji wani da ba a san ko wane ne ba na bayyana cewa “an yi sulhu da mutanen kuma za a bar su su wuce ba tare da an taɓa su ba.”

A wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun cibiyar tsaron ta Najeriya, birgediya-janar Tukur Gusau, cibiyar ta ce maƙasudin gudanar da binciken shi ne domin a tabbatar da sahihancin faifan bidiyon da kuma gano sojojin.

Sanarwar ta ƙara da cewa cibiyar na sane da cewa wasu ‘yan bindigan sun yanke shawarar tuba wanda kuma suke maraba da su.

Katsina na daga cikin jihohin da matsalar ƴan fashin daji ta yi wa katutu.

Ƴan bindigar kan sace mutane tare da yin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, haka nan suka fasa tarwatsa ƙauyuka da sacatr kayan masarufi da dabbobi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin sojoji suna ƙokarin murƙushe masu aikata laifi a yankuna daban-daban na ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *